Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe hakimi wani kauyen Niger, sun sace mutum 17

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe hakimi wani kauyen Niger, sun sace mutum 17

Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun kashe hakimin Rumache da ke yankin Kukoki na karamar hukumar Shiroro a jihar Niger, Mallam Ahmad Yakubu Rumache sannan sun yi garkuwa da mutane 17 a garuruwa hudu a karamar hukumar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai mamaya kauyen da misalign karfe 2:00 na daren jiya Alhamis.

Har ila yau yan fashin sun kwace wa mazauna kauyukan muhimman kayayyakinsu kafin suka cinna wa gidajensu wuta.

An kuma ruwaito cewar sun sace dan hakimin kauyen da suka kashe.

Harin na zuwa ne yan sa’o’i bayan lamari makamancin haka ya faru a kauyukan Magami, Gungu, Zongoro da Masuku da ke karamar hukumar Shiroro ina aka yi garkuwa da mutane 17.

An tattaro cewa mazauna kauyen da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga da wasu makamai masu hatsari da aka yi amfani dasu wajen kai hare-haren.

KU KARANTA KUMA: Ihedioha: PDP ta sake haduwa da babban cikas yayinda babban jigonta ya koma APC

Shugaban karamar hukumar Shiroro, Mallam Suleiman Dauda Chukuba ya tabbatar da hare-haren.

Ya ce an kaiwa mazauna kauyen harin ne a bazata sannan abu mawuyaci ne gano adadin yan bindigan da suka farma kauyen.

Ya bayyana cewa yan sanda daga yankin Erena da wasu yan sa-kai na nan suna kakkabe jejuna da kauyuka.

Shugaban karamar hukumar ya roki gwamnati da ta yi gaggawan kawo doki cewa karamar hukumar Shiroro bata bukatar komai face addu’a da agajin gwamnati.

Daya daga cikin yaran marigayi hakimin kauyen, Al-Mustapha Ahmed ma ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa inda ya nuna alhini kan harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel