Ihedioha: PDP ta sake haduwa da babban cikas yayinda babban jigonta ya koma APC
Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu ta sake haduwa da wani katon cikas kasa da sa’o’i 48 bayan ta rasa kujerarta na gwamna a jihar Imo.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon mataimakin jami’in binciken kudin jam’iyyar na kasa, Cif Regis Uwakwe, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Yayinda ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, a Owerri, Cif Uwakwe ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar komawa APC ne biyo bayan lamarin siyasa da ake ciki yanzu haka a jihar Imo bayanya tuntubi iyalansa da abokan siyasarsa.
Ya ce: “Ina daga cikin bangaren Ali Modu Sheriff na PDP, tare da sabon gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodinma, yayinda rikicin ya cigaba.
Sai dai kuma abun bakin ciki ne ganin cewa tsohon gwamnan da aka tsige, Cif Ihedioha, bai bi ka’idar yarjejeniyar mu ba sannan bai ba ko mutum guda daga cikinmu mukami ba, a dan kankanin lokacin da ya yi yana mulki.”
Legit.ng ta tattaro cewa yayinda ya ke sharhi kan hukuncin kotun koli, tsohon jigon n PDP ya bayyana cewa tunda hukuncin kotun koli ne karshe, ya zama dole jama’a su aminta dashi.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Shugaban DSS a Benue
“Kamar yadda nake fada wa mutane a koda yaushe kan su marawa Gwamnan jihar Imo baya tare da yi masa addu’a, hakan nake yiwa Sanata Hope Uzodinma.
“Kasancewar nayi aiki sosai tare da Sanata Uzodinma, Ina da tabbacin cewa yana da abunda ake bukata don jagorantar jihar."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng