Yau a tarihi: 'Ghana must go' ranar da aka fitittiki mutane milyan 2 daga Najeriya
'Ghana Must Go' wani shahrarren kalma ne da yasamo asali a ranar 17 ga watan Junairu, 1983 inda shugaban kasan Najeriya, Shehu Shagari, ya bada umurnin fitittikan baki daga kasar.
Shagari ya bada umurnin koran dukkan baki da basu da takardun kwarai ko kuma a garkamesu.
Ya bada umurnin ne bisa ga rikicin addinin da ke faruwa a kasar a shekarar 1980 musamman a jihar Kano.
Kimanin mutane milyan biyu, maza, maata da yara aka kora daga Najeriya. Yawancinsu yan kasashen Afrika ta yamma ne musamman yan kasar Ghana. [Wikipedia]

Asali: Facebook
Ga jerin abubuwan da suka faru a rana irin ta yau:
1983: An fitittiki baki daga Najeriya
1873 Ranar da mayakan Modoc sunka samu nasara kan Sojin Amurka a yakin Modoc
1946 Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya tayi ganawarta na farko
1991 Ranar da Amurka ta kai harin Bam Iraki lokacin yakin kasashen larabawa
1942 Ranar da aka haifi shahrarren da damben turawa, Muhammad Ali
KU KARANTA: Gwamna Zulum ya samu lambar yabon Musulmi mafi kokari a Najeriya, Pantami yazo na biyu
Mun kawo muku rahoton cewa a ranar 5 ga Nuwamban 2019, kungiyar masu siyar da kayan wutar lantarki ta kasar Ghana ta garkame shagunan bakin haure, ganin cewa sun take dokar kasar.
A kalla shaguna 50 na 'yan Najeriya aka garkame a Opera Square da ke tsakiyar Accra, babban birnin kasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayar da rahoto.
A makon da ya gabata ne kungiyar ta ba masu shaguna da ba 'yan kasar ba wa'adin rufe shagunansu zuwa watan Nuwamba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng