Yanzu-yanzu: Za'a yi aikin Hajji bana - Gwamnatin kasar Saudiyya
Gwamnatin kasar Saudiyya ta yanke shawarar gudanar da aikin Hajji wannan shekarar amma da kayyadadden adadin yan kasashe daban-daban dake zaune cikin kasar yanzu, Saudi Gazette ta ruwaito.
A wani takarda da aka saki ranar Litinin, ma'aikatar Hajj da Umrah tace: "Dubi ga yadda annobar Coronavirus ke cigaba da gudana da kuma hadarin yaduwarcutar a wuri mai tarin jama'a, an yanke shawarar gudanar da hajjin wannan shekarar (1441 H/ 2020 AD) da kayyadaddun maniyyara yan kasashe daban-daban dake zaune a Saudiyya yanzu."
An yanke shawarar haka ne domin tabbatar da cewa an gudanar da hajji cikin kwanciyar hankali da tsaro kuma za'a tabbatar da cewa an bi dokoki.
Ku saurari cikakken rahoton...

Asali: UGC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng