Satifiket ya sa Alkali ya tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga kujerarsa a Majalisar Dattawa

Satifiket ya sa Alkali ya tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga kujerarsa a Majalisar Dattawa

Yanzu nan mu ka samu labari cewa Alkali ya tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga kan kujerar da ya ke kai a Majalisar dattawan Najeriya.

Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Kubwa, ya ba Ifeanyi Ubah rashin gaskiya a shari’ar da ake yi game da zaben Sanatan.

Mai shari’a Bello Kawu, ya tabbatar da hukuncin da aka yi a bara na cewa a karbe nasarar da aka ba Sanatan na YPP a zaben 2019.

An samu Sanata Ifeanyi Ubah da laifin amfani da jabun takardar shaidar jarrabawa ta NECO wajen shiga takarar ‘Dan majalisa.

Ifeanyi Ubah ya daukaka kara ne a kotun, ya na neman ayi fatali da rashin gaskiyar da aka ba shi a wani kotu, amma bai yi nasara ba.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan PDP ya yi magana bayan kotu ta tsige shi

A hukuncin da Mai shari’a Bello Kawu ya zartar a Ranar 17 ga Watan Junairu, 2020, ya samu Sanatan da laifin da ake zarginsa.

Kawu ya bukaci hukumar zabe na kasa watau INEC ta karbe takardar shaidar lashe zaben da ta ba Sanatan na Kudancin Anambra.

Alkalin ya kuma bukaci INEC ta mika takardar nasara ga ‘Dan takarar jam’iyyar PDP, Dr. Obinna Uzoh, wanda ya zo na biyu a zaben.

Ubah shi ne mai wakiltar mazabar Anambra ta Kudu a karkashin jam’iyyar adawa ta YPP, wanda ta ke da kujera guda majalisar kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel