Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya bayyana kudurinsa na bawa Amotekun mutane miliyan 1

Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya bayyana kudurinsa na bawa Amotekun mutane miliyan 1

- Shugaban mutanen Biafra, Nnamdi Kanu yace a shirye IPOB take don goyon bayan Amotekun

- Ya jinjinawa gwamnonin Kudu maso yamma a kan sabon salon tsaro da suka kirkiro na shawo kan matsalar da ta addabi yankin

- Kanu ya tabbatar da cewa duk da rashin jituwar dake tsakaninsu da yankin, zasu tallafawa sabon salon tsaron da mutane miliyan daya

Shugaban mutanen yankin Biafra wadanda aka fi sani da IPOB, Nnamdi Kanu, a ranar Alhamis ya jinjinawa gwamnonin Kudu maso yamma da suka kirkiro da tsaro na Amotekun.

Kanu ya bayyana cewa a shirye yake don goyon bayan Amotekun kuma duk mambobin IPOB zasuyi hakan.

A wata takarda da mai magana da yawun IPOB din, Emma Powerful ya fitar, Kanu yace a shirye yake don goyon bayan sabon salon tsaron Kudu maso yamma da mutanen shi miliyan daya.

Kamar yadda Kanu yace: "Mutanen Biafra zasu goyi bayan sabon salon tsaron na Amotekun da duk karfinmu.

"Duk da tarihin kiyayyar siyasa da ke tsakanin yankin gabas din da kudu, shugabanninmu sun tabbatar da zasu yi aiki tare da shugabannin kasar Yarbawa kamarsu Pa Ayo Adebanjo, Yinka Odumakin, Femi Fani-Kayode da Omoyele Sowore.

KU KARANTA: Allah Sarki: Dan shekara 14 ya bayyana yadda ya sayar da kodarshi domin ya biyawa kanshi kudin makaranta

"Zan goyi bayan yarbawan da suka kafa Amotekun. IPOB zata yi aikin hadin guiwa dasu. Idan mutane miliyan daya suke so zan basu don tabbatar da an datse kisan da Fulani keyi a yankin. Zamu goyi bayan Yarbawan ta kowanne bangare don ganin mun kawo karshen Fulanin.

"IPOB zata bi bayan Amotekun. Babu inda Amotekun zata tafi don sun zo zama ne."

Idan zamu tuna, IPOB cikin kwanakin nan ne ta jinjinawa gwamnonin Kudu maso gabas da suka kafa sabon salon tsaro mai suna Amotekun.

Jaridu sun bayyana cewa gwamnonin jihohin Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Ekiti da Legas sun hadu a Ibadan inda suka kaddamar da Amotekun.

Gwamnonin sun bayyana cewa an kirkiro Amotekun ne don shawo kan matsalar tsaro a yankin Kudu maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel