Saurayina ya sayar dani ga wasu mutane N300,000 domin su dinga iskanci dani

Saurayina ya sayar dani ga wasu mutane N300,000 domin su dinga iskanci dani

- Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ta jihar Legas ta gano wata kungiyar safarar 'yanmata zuwa kasashen waje don karuwanci

- An gano wani gini a yankin Iyana-Ipaja dake a jihar Legas inda ake tare 'yan matan kafin a turasu kasashen duniya

- Daya daga cikin 'yan matan ta bayyana cewa saurayinta ne ya siyar da ita don a tura ta karuwancin

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ta jihar Legas sun gano wani gini a yankin Iyana-Ipaja dake jihar Legas inda ake aje kananan 'yan mata kafin ayi safararsu zuwa Mali da sauran sassa na duniya don karuwanci.

Shugaban kungiyar Omowunmi Michael mai shekaru 30 ta shiga hannu tare da yara mata masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24. Sunansu Alaoye Joy mai shekaru 22, Victoria Oshioke mai shekaru 18, Amaka Eze mai shekaru 23 da kuma Anuoluwapo Mustapha.

Jaridar Vanguard ta gano cewa an kama shugaban kungiyar ne da sauran mambobin bayan sun samu hatsaniya a kan nawa za a raba a kudin siyar da 'yanmatan.

Daya daga cikin 'yan matan mai suna Osioke ta bayyana cewa saurayinta ne ya fara siyar da ita zuwa kasar Mali lokacin tana da shekaru 16. "Saurayina ya siyar dani a kan CEFA 500,000 kuma an kaini Mali inda aka dinga tirsasa ni ina kwantawa da maza daban-daban.

KU KARANTA: Ya kashe matarsa da 'ya'yansa guda uku ya kulle kanshi dasu a daki na tsawon mako uku

"Na dawo bayan shekaru biyu. Maxwell ya kirani yace inje Benin. Na same shi amma sai yace yana son in koma Mali. Na nuna rashin amincewata amma sai ya koreni cikin dare. Saboda tsananin tsoro sai na amince inda yasa ni a bas zuwa Legas. Nayi farin ciki da Ubangiji ya tona musu asiri. Za a tseratar dani daga wata azabar", tace.

Shugaban hukumar NSCDC din ya ja kunnen 'yan mata a kan masu yi musu alkawarin ayyuka a wajen kasar nan. Yayi kira ga iyaye da su guji fadawa cikin wannan tarkon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel