APC na da kyakyawar makoma a Kudu maso gabas - Ohanaeze

APC na da kyakyawar makoma a Kudu maso gabas - Ohanaeze

- Kungiyar Ohanaeze Ndigbo tace akwai yuwuwar jam'iyyar APC ta mamaye jihohin kasar Ibo kafin zaben 2023

- Babban sakataren kungiyar ta kasa, Uche Okwukwu ya sanar da hakan ne yayin mika sakon taya murnar da yayi ga sabon gwamnan jihar Imo

- Sakon taya murnar daga Ohanaeze yazo ne kasa da sa'o'i 24 bayan kotun koli ta bayyana cewa dan siyasar haifaffen kasar Ibo a matsayin gwamnan jihar Imo

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo a ranar Laraba ta ce akwai yuwuwar jam'iyyar APC ta mamaye jihohin kasar Ibo kafin zaben 2023, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Babban sakataren kungiyar ta kasa, Uche Okwukwu, ya sanar da hakan a sakon taya murna da yayi ga sabon gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a kan nasarar da yayi a kotun koli. Ya kwatanta shari'ar da daidaitacciya kuma cancantacciya.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta ce za ta binciki gwamnonin da suka yi ruf-da-ciki da kudaden kananan hukumomi

Okwukwu yayi bayanin cewa nasarar Uzodinma ta haifar da farin ciki ga Ndigbo ta yadda APC ta fara mamaye kasar Ibo din.

Sakon taya murnar daga Ohanaeze yazo ne kasa da sa'o'i 24 bayan kotun koli ta bayyana cewa dan siyasar haifaffen kasar Ibo din ya zama wanda yayi nasara a zaben 2019 na jihar Imo.

Okwukwu yace, "Ohanaeze na taya Sanata Hope Uzodinma a kan nasararsa a kotun kolin Najeriya. Wannan hukuncin cancantacce ne. Ndigbo na matukar farin ciki da aka dawowa da jama'ar jihar Imo hakkinsu da burinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel