Bidiyon Okorocha da ahlinsa yayinda suke bikin tsige Ihedioha daga matsayin gwamna

Bidiyon Okorocha da ahlinsa yayinda suke bikin tsige Ihedioha daga matsayin gwamna

- Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sadarwa ya nuno Sanata Rochas Okorocha tare da iyalansa suna rawa suna murna

- Anyi zargin cewa tsohon gwamnan na Imo da iyalan nasa na murnar tsige Emeka Ihedioha daga matsayin gwamnan jihar Imo da kotun koli tayi

- Ba a tabbatar da sahihancin bidiyon ba saboda baya dauke da ranar da aka yi shi

Wani bidiyo da ba a tabbatar ba ya billo a shafukan sadarwa inda aka nuno Sanata Rochas Okorocha na murna da waka tare da iyalansa kan zargin tsige Emeka Ihedioha daga matsayin gwamnan jihar Imo da kotun koli tayi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa bidiyon ya nuna “sha’ani na ibada da godiya” yayinda Okorocha da ahlinsa baki daya suka yi murnar nasarar Sanata Hope Uzodinma kan Emeka Ihedioha, bayan hukuncin kotun koli kan zaben gwamna na 2019 a jihar.

A bidiyon wanda wata mai amfani da shafin Twitter, @Lailaijeoma ta wallafa, An gano Okorocha tare da matarsa da sauran ahlinsa suna waka, tafi da rawa.

Sai dai kuma, kai tsaye Legit.ng ba za ta iya tabbatar da ko da gaske bidiyon na nuna Okorocha da ahlinsa ne a lokacin da suke murnar tsige Ihedioha ne.

Wasu masu amfani da shafukan sadarwa sun yi ikirarin cewa tsohon bidiyo ne sannan cewa Okorocha da ahlinsa ba bikin nasara a kotun koli suke yi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng