YCE: A kan me za a haramta aikin Amotekun yayin da wasu Makiyaya su ke barna

YCE: A kan me za a haramta aikin Amotekun yayin da wasu Makiyaya su ke barna

Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya jawo wasu manya sun kai ga gargadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata kungiya ta manyan majalisar dattawan Yarbawa watau YCE ta maidawa kalaman da Ministan shari’ar ya yi kwanan nan martani.

Abubakar Malami, ya fito ya yi jawabi ya na cewa Dakarun Sojojin Amotekun da aka kafa a Kudancin kasar ba su da hurumin aiki.

Kanal Ade Agbede (mai ritaya) ya yi magana a madadin kungiyar YCE inda ya yi tir, ya ce akwai tsokanar fada a cikin kalaman Ministan.

YCE ta bakin Ade Agbede, ta ce bai kamata irin wadannan kalamai su fito daga bakin mai rike da babban ofishi kamar Ministan shari’a ba.

KU KARANTA: Shugabannin kasar Yarbawa sun yi wa Ministan shari'a rubdugu

Kungiyar ta nuna goyon bayanta da cewa: “Amotekun aikin Yarbawa ne, kuma gwamnonin Yarbawa sun samu albarkar kowane 'Da."

“Abin mamaki ne ace yunkurin da ake yin a tsare rayuka da dukiyoyin jama’an da su ka zabi gwamnoni bai halatta ba.” Inji YCE.

YCE ta kara da cewa: “A daidai wannan lokaci yayin da Makiyayan da ke kashe mutane su na ta’adi, su ke yawo a Gari ana ji ana gani.”

Irin su Wole Soyinka da Femi Falana sun soki wannan matsaya. Haka zalika wani gwamnan Kudu ya ce Ministan ya fita daga huruminsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel