Harin sarkin Potiskum: An kashe mutane 30, anyi awon gaba da 100

Harin sarkin Potiskum: An kashe mutane 30, anyi awon gaba da 100

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 15 ga Junairu, Premium Times ta ruwaito.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya ce mutane shida kadai aka kashe kuma biyar sun jikkata. Ya tabbatar da cewa an yi awon da wasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Amma manyan majiyoyi a hukumar sun bayyanawa manema labarai cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 30 da safiar Laraba.

Mun kawo muku rahoton cewa Wasu yan bingida sun kaiwa mai martaba sarkin Patiskum, Alhaji Umaru Bubaram, inda suka kashe fadawansa uku a babban titin Kaduna zuwa Zariya.

An bayyana cewa Sarkin na kai ziyara masarautun Arewacin Najeriya ne cikin shirye-shiryen kaddamar sabon Masallacin Patiskum da aka shirya yi ranar 18 ga watan Juaniru, 2020.

Yana hanyarsa ta tafiya Zariya ne yan bindiga suka budewa motarsa wuta.

Harin ya faru ne misalin karfe biyun dare a kauyen Fandatio, kusa da Maraban Jos.

Ba'a sani ko Sarkin musamman sukayi kokarin kaiwa hari ba amma Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya shafi wasu matafiya daban.

Daya daga cikin makusantan sarkin, Sarkin Yamman Patiskum, Alhaji Gidado Ibrahim, ya tabbatar da labarin a asibitin Barau Dikko da aka garzaya da sarkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel