Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce

Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce

- Wani Injiniya mai suna Ameh Osivue Shagari ya wallafa hotunan Gwamna Zulum tare da shi a kujerar gama-gari a jirgin sama

- Injiniyan yaci karo da gwamnan jihar Borno din ne a cikin jirgin sama daga Abuja zuwa Maiduguri a ranar Talata

- Kamar yadda ya wallafa, hira kan siyasar Najeriya da ta APC ta tsinke tsakaninsa da gwamnan

Wani Injinya mai suna Ameh Osivue Shagari ya wallafa hotunan gwamna jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a yayin da yake zaune a cikin jirgin sama kuma kujerar gama-gari daga Abuja zuwa Maiduguri a ranar Talata, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Wani fasinja mai suna Abacha Nawaisu, wanda suka hau jirgi daya da gwamnan, ya wallafa hotunan gwamnan yana tattaki zuwa kujerarsa.

Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce
Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce
Asali: Facebook

Kamar yadda Osivue Shagari ya wallafa, “a yau ne na hau jirgi daya kuma kusa da kujerar gwamna Zulum daga Abuja zuwa Maiduguri. A take kuwa hira ta tsinke tsakanina da shi a kan siyasar Najeriya da ta jihar Edo. Abu na farko da ya ja hankalina zuwa gwamnan shine yadda ya siya kujerar gama-gari. Ba kamar yadda gwamnan jihata ya saba ba. Ya sanar dani cewa yana goyon bayan Bulama wanda ke neman sakataren APC na kasa a kan Mustapha wanda yake neman wannan matsayin. A lokacin da muka kai Maiduguri, ya bukaci in shiga tawagarsa don mu cigaba da hirarmu.”

Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce
Hawan kujerar jirgi 'gama-gari' da Gwamna Zulum yayi ya jawo cece-kuce
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel