INEC ta bawa Uzodinma na APC shaidar lashe zaben kujerar gwamnan Imo

INEC ta bawa Uzodinma na APC shaidar lashe zaben kujerar gwamnan Imo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bawa Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC shaidar samun nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Imo.

INEC ta bashi takardar shahadar ne ranar Laraba, kasa da sa'o'i 24 bayan kotun koli ta soke zaben Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo.

A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP tare da tabbatar da Hope Uzodinma, dan jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Da farko INEC ta bayyana cewa ba zata bawa Sanata Hope Uzodinma, na jam'iyyar APC, shaidar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Imo ba har sai ta samu takardar umarnin yin hakan daga kotun koli.

INEC ta bawa Uzodinma na APC shaidar lashe zaben kujerar gwamnan Imo
Yayin bawa Uzodinma na APC shaidar lashe zaben kujerar gwamnan Imo a ofishin INEC
Asali: UGC

A wani jawabi da Rotimi Oyekanmi, sakataren yada labaran shugaban INEC ya fitar, ya ce, "har yanzu hukumar INEC bata samu rubutaccen sako daga kotun koli ba a kan hukuncin data yanke, saboda haka ba zamu iya bawa dan takarar APC takardar shaidar lashe zabe ba. Sai dai, da zarar mun samu sakon kotun, zamu bashi takardar shaidar."

Kazalika, ya bayyana cewa rashin bashi takardar shaidar ba zai hana rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Imo ba.

DUBA WANNAN: Binciken wayar hannu: Matashi ya kone budurwarsa kurmus bayan ganin wani faifan bidiyo a wayarta

Oyekanmi ya kara da cewa hukumar INEC mai biyayya ce ga hukunci da kuma umarnin kotu, amma duk da haka ba zata iya dogaro da labaran jaridu ba wajen daukan wani mataki, dole sai an bata kwafin takardar hukunci mai dauke da hatimi da sa hannun mahukuntan kotun koli kafin ta bayar da shaidar cin zaben (CoR).

Mika takardar shahadar ga Uzodinma tamkar tabbaci ne a kan cewa INEC ta samu sako daga kotun koli a kan hukuncin da ta zartar ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel