Shehu Sani: Danyen aikin da ka yi a baya ne ya dawo maka – Lauretta Onochie

Shehu Sani: Danyen aikin da ka yi a baya ne ya dawo maka – Lauretta Onochie

Lauretta Onochie wanda ta na cikin Hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta tofa albarkacin bakinta game da binciken Shehu Sani.

A cewar Lauretta Onochie wanda ta ke taimakawa shugaba Buhari, binciken da ake yi wa Shehu Sani, ya nuna cewa akwai abin da ya ke boyewa.

Tun kwanakin baya hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta tsare tsohon Sanatan bisa zargin kwacen kudi.

Mai taimakawa Shugaban Najeriya, ta ce mutanen da su ka saba surutan banza, su ne su ke kawo tasgaro wajen yakar cin hanci da rashawa a kasar.

Onochie wanda ta ke bada shawara wajen harkar yada labarai a dandalin sadarwan zamani ta ce zunuban irin wadannan mutane ya dawo ya ci su.

KU KARANTA: Sukar Gwamnatin Buhari ta sa EFCC ta kama ni - Shehu Sani

A jawabin da Onochie ta yi a kan dandalin Tuwita, ta bayyana cewa EFCC ba su bukatar jagora wajen damke Shehu Sani saboda barnar da ya yi.

“Na dade ina da ra’ayin cewa wadanda su ke kwaratsin banza a kasar nan, su na cikin masu hana ruwa guda wajen yakar Barayi.” Inji Hadimar.

Misis Onochie ta sa wa tafiyar Shehu Sani da ire-irensa sunan #CorruptionFightingBack Association Of Nigeria watau kungiyar CoFiBa.

A Ranar 13 ga Watan Junairu, Hadimar ta ce: “Hukumomin yaki da barayi irinsu EFCC ba su bukatar su waiwayesu, zunubansu, za su nuna su.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel