Asirin wata budurwa ya tonu da take amfani da jinin al'adarta tana dafawa saurayinta abinci

Asirin wata budurwa ya tonu da take amfani da jinin al'adarta tana dafawa saurayinta abinci

- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta cafke wata budurwa mai suna Ijeoma da laifin yi wa saurayinta girki da jinin al'adarta

- Saurayin ya ce mutuniyar arziki ce da farko amma yanzu har karuwanci take taba wa kuma ya taba kamata da kan shi

- Ijeoma ta amsa laifinta amma tace wata kawarta ce ta bata shawarar hakan don kada saurayin nata ya barta

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta cafke wata budurwa mai suna Ijeoma a kan zarginta da ake da amfani da jinin al'adarta don yi wa saurayinta girki. Da farko ta musanta amma daga baya ta amsa laifinta tare da tabbatar da cewa tayi amfani da jinin na tsawon watanni bakwai tana yi mishi girki don kada ya barta.

Saurayi mai suna Kingsley wanda shine saurayin Ijeoma yace, "na hadu da ita shekaru uku da suka gabata. Bayan soyayyar mu ta fara nisa ne na gano tana cin amanata kuma ta fada karuwanci. Na taba kamata da wani tsoho a otal amma na yafe mata saboda ta nuna nadamarta a fili. Abokai na masu tarin yawa suna fada min cewa budurwata karuwa ce amma naki ji saboda ina sonta.

"A ranar Juma'a da ta gabata ne muka yi fada amma abin mamaki sai naji tana waya tare da tambayar yawan jinin al'adar da zata yi amfani dashi wajen yi min girki."

KU KARANTA: Asiri ya tonu: An kama shugaban makaranta da yake iskanci da wasu daliban shi tagwaye

Ta musanta ikirarin saurayinta amma bayan 'yan sandan sun binciketa, sai ta amsa cewa tayi amfani dashi na watanni bakwai ne.

A kalamanta "bana yin asiri, ban san wani boka ba. Kawai ina kaunar saurayina ne sosai ba kadan ba kuma bana son ya barni. Wata kawata ce ta ce idan ina amfani da jinin al'ada wajen yi mishi girki toh zai kaunace ni. Kuma inayi yana amfani. Bani da niyyar kashe shi, kaunar shi nake yi."

A lokacin da aka tambayeta ko tana karuwanci, sai tace "inayi lokaci zuwa lokaci. Da kudin nake kula da kannaina biyu dake jami'a. Bana so in takura saurayina a kan karatun kannaina shiyasa nake karuwanci."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Andrew yace "muna cigaba da binciken lamarin kuma idan saurayin yaso a mika ta kotu, zamu kaita a yanke mata hukunci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel