Gwamna El-Rufai ya nada sabon shugaban hukumar KASTLEA

Gwamna El-Rufai ya nada sabon shugaban hukumar KASTLEA

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya amince da nadin Manjo Garba Yahaya Rimi mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar kula da dokokin hanya ta jahar Kaduna, KASTLEA.

Rahoton Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mashawarcinsa na musamman a kan harkokin watsa labaru, Muyiwa Adekeye a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, inda yace ya nada shi ne saboda kwarewarsa.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar ‘matasan tsaro na yarbawa’ a matsayin haramtacciya

Bugu da kari gwamnan ya bayyana nadin Manjo Rimi ya fara ne nan take. Sanarwar ta kara da cewa kafin wannan sabon matsayi, Manjo Rimi ne mataimakin babban manaja na hukumar kasuwa mai kula da tsaro.

Haka zalika sabon shugaban na KASTLEA ya taba kasancewa shugaban sashin tsaro na majalisar yakin neman zaben gwamnan Nasir Ahmad El-Rufai a shekarar 2014, daga bisani ya zama sakataren sashin komai da ruwanka nay akin neman zaben.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana rundunar tsaro na sa kai da gamayyar gwamnatocin jahohin kudu masu yammacin Najeriya, watau yankin yarbawa suka kafa mai suna ‘Amotekun’ a matsayin haramtacciyar rundunar tsaro.

Babban lauyan gwamnati, kuma ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace aikin tabbatar da tsaro aiki ne na gwamnatin tarayya ita kadai.

“Kafa wani rundunar tsaro mai suna Amotekun bai halasta ba, kuma ya saba ma tanadin dokokin Najeriya, kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya samar da rundunar sojan kasa, sojan ruwa, sojan sama, Yansanda da kuma sauran hukumomin tsaro daban daban da zasu taimaka ma wajen tsaron Najeriya.

“Don haka babu wata jaha ita kadai ko a kungiyance dake da iko ko hurumin kafa wani rundunar tsaro da zai kare Najeriya ko kuma wani sashi na kasar, wannan kuma sashi na 45 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tabbatar da haka.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel