Hannan Buhari: Amfani da jirgin shugaban kasa ya saba doka - Inji Falana

Hannan Buhari: Amfani da jirgin shugaban kasa ya saba doka - Inji Falana

Fitaccen Masanin shari’ar nan, kuma gawurtaccen Mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana, ya maida martani ga fadar shugaban kasa.

Femi Falana ya yi raddi ne ga kalaman da Mai magana da yawun bakin shugaban kasa watau Graba Shehu ya yi a game da Hannan Buhari.

Malam Shehu ya fito ya na kare ‘Diyar shugaban kasar bayan ta yi amfani da jirgin gwamnati wajen yin wasu sabgoginta, ya ce ba ta yi laifi ba.

Sai dai Femi Falana SAN, ya bayyana cewa sam bai halatta ‘Diyar shugaban kasar Najeriyar ta yi amfani da jirgin fadar shugaban kasa ba.

Asali ma gawurtaccen Lauyan ya ba shugaban kasa shawara ya raba Iyalinsa daga yawo a cikin jiragen fadarsa wajen yin ayyukan gabansu.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Hannan Buhari a jirgin Shugaban kasa

Hannan Buhari: Amfani da jirgin shugaban kasa ya saba doka - Inji Falana
Lauya ya ce bai kamata 'Ya 'yan Buhari su rika yawo a jirgin shugaban kasa ba
Asali: UGC

Falana ya yi wannan magana ne a wani jawabi da ya fitar a Ranar 12 ga Watan Junairu, inda ya ce doka ba ta Hannan damar taba jirgin ba.

“Kai babu wanda ya taba maida jirgin fadar shugaban kasa tamkar na shi a tarihin Najeriya.”

“Wannan batun da ake yi na cewa an saba ganin Iyalin shugabanni su na amfani da jirgin fadar shugaban kasar bai da daurin gindi a doka.”

Lauyan ya ce babau wata doka ko tsari da ya halattawa Iyalin shugaban kasa hawa jirgin da ke cikin fadarsa domin yin aikace-aikacen gabansu.

A karshe Lauyan ya bayyana cewa amfani da jiragen kasar wajen biyan bukatun kai zai rage kudin da gwamnati ta ke facaka da su a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel