Ziyarar Osinbajo: A kullum muna maraba da zuwanka jahar Kano – Sarkin Kano

Ziyarar Osinbajo: A kullum muna maraba da zuwanka jahar Kano – Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya yi maraba da ziyarar aiki na yini daya da mataimakin shugabankasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai jahar Kano a ranar Litinin, 13 ga watan Janairu.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da Osinbajo ya kai masa gaisuwar ban girma a fadarsa dake cikin birnin Kano, inda yace Osinbajo ya dauki jahar Kano tamkar gidansa, don haka a kullum suna maraba da zuwansa.

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun taya Dahiru Bauchi alhinin rashin matarsa

Daily Trust ta ruwaito Osinbajo ya kai ziyarar ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka guda biyu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta aiwatar da suka hada da gadar sama ta Alhassan Dantata dake Sabon Gari da kuma gadar Tijjani Hashim dake kofar Ruwa.

Haka zalika Osinbajo ya gudanar da aikin sanya tubalin wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Gwamna Ganduje za ta gudanar a jahar. A jawabinsa, Sarki Sunusi ya bayyana farin cikinsa da ziyarar Osinbajo, inda yace hakan ya nuna muhimmancin jahar Kano ga gwamnatin tarayya.

Haka zalika Sarkin ya yaba ma Gwamna Abdullahi Ganduje bisa ayyukan cigaban da yake gudanarwa a jahar domin amfanin jama’anta, inda ya bayyana ayyukan a matsayin cigaba da zasu inganta rayuwar jama’a tare da habbaka tattalin arzikin jahar.

Shi ma da yake nasa jawabin, Farfesa Osinbajo ya jinjina ma Sarki Sunusi bisa kokarin da yake na tabbatar da zaman lafiya a jahar, sa’annan ya yaba ma Sarkin bisa kokarin da yake yin a tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mabanbanta kabilun jahar.

Daga karshe ya tabbatar ma Sarkin da cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da baiwa jahar Kano kulawa na musamman wajen samar da ayyukan cigaba, fiye da sauran jahohin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel