Kama Zakzaky: Akwai ranar kin dillanci – Yan Shi’a ga Gwamna El-Rufai

Kama Zakzaky: Akwai ranar kin dillanci – Yan Shi’a ga Gwamna El-Rufai

Y’ayan babbar kungiyar yan Shi’a a Najeriya, watau kungiyar yan uwa Musulmi ta Najeriya, IMN, sun yi kira tare da jaddada gargadi ga gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, inda suka ce masa ya kiyayi ranar sakamako.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu a garin Kaduna, inda yace babu wani barazana da gwamnati za ta musu da zai hana su neman adalci.

KU KARANTA: Badakalar $24000: Ba zan taba yin shiru wasu na fadin karairayi a kai na ba – Shehu Sani

Sanarwar yan Shian ya fito ne a matsayin martani ga jawabin da gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi cikin wata tattaunawa da ya yi da yan jarida a ranar Juma’a, inda yace suna sharia da Zakzaky ne bisa laifukan da shi da mabiyansa suka aikata tsawon shekaru 30 a Zaria.

“Don haka duk ihun da mutum zai yi, duk zanga zangar da wasu za su yi a kan Zakzaky ba zai sa mu taba sakin sa ba har sai kotu ta yanke hukunci a kansa, kuma na yi alkawarin zartar da duk hukuncin da kotu ta yanke masa.” Inji Gwamna El-Rufai.

Sai dai cikin martaninsa, shugaban sashin watsa labaru na IMN, Ibrahim, yace za su cigaba da gudanar da zanga zangar lumana har sai an yi musu adalci, musamman shugabansu Ibrahim Zakzaky, da mabiyansa dake hannun hukuma, da kuma mabiyansu da aka kashe a watan Disambar 2015.

A wani labarin kuma, Wani mutumi da zarginsa da tabin hankali, Badejo Adewale ya banka ma wani abokin zaman sa, Bolatito Kadara wuta a unguwar Surulere na jahar Legas a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace mahaukacin ya wawwatsa ma Kadara fetir, daga nan sai ya cinna masa wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel