Mutuncin rundunar sojojin Najeriya ya zube - Gwamna Wike

Mutuncin rundunar sojojin Najeriya ya zube - Gwamna Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya ta rasa duk wata kima da take da ita saboda ta bari ana amfani da ita domin yin magudin zabe a cikin kasa.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya halarci Coci domin bikin ranar tunawa da gudunmawar mazan jiya.

A cewar gwamnan, 'yan Najeriya ba zasu karrama dakarun sojojin da ake hada baki da su domin tafka magudin zabe ba.

"Ba zamu karrama dakarun soji da basu da kwarewar aiki ba kuma ake hada baki domin satar akwatin zabe ba. Ina kira ga rundunar sojojin Najeriya da ta koma turbar gaskiya ta hidimta wa kasa.

"Abin takaici ne ganin yadda mutuncin rundunar soji ya zube saboda halayyar wasu marasa kishi da kware wa daga cikinsu.

Mutuncin rundunar sojojin Najeriya ya zube - Gwamna Wike
Nyesom Wike
Asali: Depositphotos

"Babu wanda yake tsoron sojoji yanzu saboda rashin kwarewar aiki da suke nuna wa.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Sai bayan shekara daya da mutuwar mijina aka sanar dani - Matar soja

"An yi amfani da su wajen tafka magudin zabe a jihar Ribas, kuma sun kashe mana mutane, ba zamu taba tuna wa dasu ba.

"Na gode wa Allah cewa shugaban hukumar INEC da kansa ya bayyana cewa jami'an tsaro ne babbar matsalar hukumar. Hakan ya tabbatar da duk abubuwan da na fada a baya," a cewar gwamna Wike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel