Rayuwa: Matashiya 'yar bautar kasa ta kashe kanta, ta bar wasiyya kafin aikata hakan

Rayuwa: Matashiya 'yar bautar kasa ta kashe kanta, ta bar wasiyya kafin aikata hakan

Wata matashya dake bautar kasa a jihar Kogi mai suna Bolufemi Princess Motunrayo ta kashe kanta ranar Juma'a.

Matashiya Bolufemi ta kashe kanta ne ta hanyar kwankwadar gora biyu ta maganin kashe kwari mai guba da aka sani da 'Snipper'.

Bolufemi, budurwa 'yar kwalisa, 'yar asalin jihar Kogi ce, kuma ta kammala karatunta ne a fannin ilimin banki da kudi a jami'ar Prince Abubakar Audu dake Ayingba, jihar Kogi.

Tana cikin rukunin 'C' na matasa 'yan bautar kasa dake aiki a makarantar sakandiren 'yammata dake garin Ibagwa-Aka a yankin karamar hukumar Igbo-Eze ta kudu a jihar Akwa Ibom.

Rahotanni sun bayyana cewa ta kashe kanta ne ranar Juma'a bayan ta bar wata wasiyya dake cewa, "wannan rayuwa bata da wani amfani."

Rayuwa: Matashiya 'yar bautar kasa ta kashe kanta, ta bar wasiyya kafin aikata hakan
Matashiya 'yar bautar kasa da ta kashe kanta
Asali: UGC

"Na kashe kaina ne saboda ban ga wani amfanin wannan rayuwar ba.

"Mummy ina sonki. Daddy ina sonka. Matthew da John, ku kula da kanku. Zamu hadu a inda ba zamu rabu ba. Ina sonku," kamar yadda Bolufemi ta rubuta a wasiyyar da ta bari.

DUBA WANNAN: Dalibai mata 5 sun yi wa malaminsu fyade a makarantar sakandire, ya suma

Wata 'yar uwa ga marigayiya Bolufemi mai suna Funke Ajayi ta tabbatar wa da manema labari faruwar lamarin tare da bayyana cewa sun yi matukar girgiza da samun labarin abin da matashiyar ta aikata.

A cewarta, marigayiyar bata nuna wata alama ta zata aikata hakan ba, saboda ko a ranar Alhamis tana cikin walwala da farinciki kamar koda yaushe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng