Badakalar N3.4bn: Gwamnatin Kano ta ki amincewa da bukatar Sarki Sanusi II a gaban kotu

Badakalar N3.4bn: Gwamnatin Kano ta ki amincewa da bukatar Sarki Sanusi II a gaban kotu

Bangaren koke da hukumar yaki da almundahanar kudade na gwamnatin jihar Kano, a ranar Alhamis ta yi kira ga babbar kotun jihar da ta soke bukatar karin duba shari'ar da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya shigar.

Sanusi ya shigar da koke a gaban kotun a kan tayi watsi da rahoton rikon kwarya na hukumar a kan zarginsa da badakalar Naira biliyan 3.4.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa, Sarkin na kalubalantar rahoton kwamitin rikon kwaryar da ke mika bukatar gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi.

Wadanda ake karar sune hukumar koke da korafi da kuma kwamishinan shari'ar na jihar Kano.

Idan zamu tuna, Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa rahoton kwamitin rikon kwaryar ya bayyana cewa, ya bankado wasu makuden kudade da masarautar jihar Kano karkashin shugabancin sarki Sanusi II, tsakanin 2014 zuwa 2017.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

A lokacin da aka taso da shari'ar a ranar Alhamis, lauyan Sanusi, A. B. Mahmud (SAN), ya roki kotun da ta ba duk bangarorin biyu damar su daidaita yanayin, bayan kin amincewa da bukatar da sarkin ya mika na kara duba shari'ar.

Lauyan hukumar, S.S Shitu (SAN), ya soki wannan bukatar tare da bukatar kotun da ta soke shari'ar.

Jastis Suleiman Baba-Namalam, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Janairu don cigaba da sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel