ASUU ta fadi warwas bayan shugaba Buhari ya tilasta suyi rijista da IPPIS

ASUU ta fadi warwas bayan shugaba Buhari ya tilasta suyi rijista da IPPIS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis, 9 ga watan Janairu, ya fada ma mambobin kungiyar malaman jami’a (ASUU) da su bayar da hadin kai a manufar yaki da rashawar gwamnati ta hanyar amincewa da manufofin dake dabaibaye da tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS.

Hakan ya kasance sakamakon ganawarsa da shugabannin kungiyar malaman a jiya Alhamis, a faar Shugaban kasa da ke Abuja.

An tattaro cewa kungiyar ta ASUU na adawa da yiwa mambobinta rijista kan tsarin IPPIS.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana IPPIS a matsayin kutse wanda ya saba ma yarjejeniyar da ke tsakanin kungiyar da gwamnati.

Sai dai shugaba Buhari a wani jawabi daga hadiminsa, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali sosai wajen inganta jami’ai da tsarin makarantun jami’a ta yadda za a dunga yaye dalibai masu inganci, kamar yadda ya ba da tabbacinn cewa daga yanzu za a ba ilimi kula na musamman a kokarin inganta kasar.

Shugaba Buhari, wanda ya karbi bakuncin shugabannin ASUU karkashin jagorancin Farfesa Biodun Ogunyemi a fadarsa, ya ce ayyukan makarantun jami’a zai taimaka sosai wajen inganta tattalin arziki, musamman idan aka mayar da hankali ga kimiya da fasaha.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta kashe hazikan sojoji 3 da yan farar hula 8 a Monguno

Shugaban kasar ya bukaci mambobin ASUU da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen cimma manufarta na inganta harkar ilimi da samun sahihan takardun shaidar kammala karatu ta hanyar ba wannan shiri hadin kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel