Duk wanda ya iya warkar dani nayi alkawarin siya mishi gida a Turai - Gurgu ya kalubalanci Fastoci

Duk wanda ya iya warkar dani nayi alkawarin siya mishi gida a Turai - Gurgu ya kalubalanci Fastoci

- Waraka, mu'ujiza da kuma karfin iko na daga cikin abubuwa kadan da fastoci a nahiyar Afirrka ke bayyana wa

- Wani mawaki mai suna Ogidi Brown dan asalin kasar Ghana ne da ya dena tafiya sakamakon hatsarin da yayi a 2015

- Ya ce duk faston da zai warkar dashi, zai mika wuya ga mu'ujizar shi kuma zai siya wa faston katon gida a Turai

Mawakin kasar Ghana, Ogidi Brown na kamfanin waka na OGB ya bukaci fastocin kasar da su zo don gwada ilhamarsu a kan shi. Ya ce yana bukatar su yi amfani da mu'ujiza wajen warkar dashi daga karayar kafafun da yake fama da ita. Shi kuwa yayi alkawarin yi wa duk wanda yayi hakan kyauta mai tsoka.

Sanannen abu ne cewa fastoci a Afirka na amfani da mu'ujiza wajen warkar da jama'a miyagun cutukan da suka addabesu.

Ogidi yace, tunda fastocin suna ikirarin sun 'ma'aika' ne daga Ubangiji, ya fitar da wannan gasar ne don gwada karfin ikonsu kuma ya san ko mu'ujizojin na aiki da gaske ba wai ikirari kawai suke yi ba.

KU KARANTA: Nafi son Kare na fiye da kowanne mutum a duniyar nan - Toke Mokinwa

Tun bayan da Ogidi yayi hatsari a 2015, baya iya tafiya kwata-kwata.

Kamar yadda ya ce, duk faston da ke ikirarin Ubangiji ne ya turo shi, toh yazo ya warkar da shi. Zai shaida tare da mika wuya ga karfin ikon wannan faston kuwa. Kuma yayi alkawarin zai siya mishi tangamemen gida a Turai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel