Yadda aka jefa almajiri cikin dakin gasa burodi ya kone a jihar Gombe

Yadda aka jefa almajiri cikin dakin gasa burodi ya kone a jihar Gombe

- Wani almajiri mai shekaru 10 a duniya na kwance rai a hannun Allah sakamakon kunar kafafuwan shi

- An zargi manajan gidan burodi da wurga shi cikin murhun gasa burodi a Bajoga dake jihar Gombe

- Bayan kama manajan da 'yan sanda suka yi, an gano cewa sun sake shi bayan belin shi da wani babban mutum yayi

Wani yaro mai shekaru 10 kacal a duniya na kwance rai a hannun Allah sakamakon mummunar kunar da yayi a kafafuwan shi. An zargi manajan gidan Burodi a garin Bajoga dake jihar Gombe da wurga yaron cikin murhun gasa Burodi.

Bayanai sun bayyana cewa, mutumin ya zargi almajirin ne da satar masa burodi.

Wata kungiya mai kare muradin talakawa mai suna Kungiyar Muryar Talaka, ta shaida wa BBC cewa, an cafke wanda ake zargin da azabtar da yaron, amma daga baya sai aka sake shi. Amma kuma yaron na kwance magashiyyan a cikin ciwo.

Daya daga cikin 'yan kungiyar dake garin Bajoga, Ahmed Sulaiman ya shaida wa BBC cewa ya ziyarci yaron da abun ya faru dashi wanda malamin allo ke jinyar shi.

Ahmed ya ce "manajan gidan burodin ya zargi yaron da satar mishi burodi, hakan yasa ya jefa shi cikin dakin gasa burodin.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mata tayi yunkurin sayarwa da matsafa dan kamfen karuwar da mijinta ya kawo gidansu

"Jim kadan sai ya fito dashi amma ganin babu abin da ya samu yaron, sai ya sake mayar da shi ciki. Bayan fitowa ne kuwa dashi kamannin yaron suka sauya."

Jagoran Muryar Talakan ya zargi cewa manajan gidan burodin ya tsira daga hannun 'yan sanda bayan da wani babban mutum ya yi belin shi.

Amma kuma, a lokacin da BBC ta tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Gombe, SP Mary Malum ta ce ba ta da bayani amma idan sun sami bayani za su sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel