Dalibai 5 mata sun yi wa malaminsu a makarantar sakandire fyade, ya suma

Dalibai 5 mata sun yi wa malaminsu a makarantar sakandire fyade, ya suma

Mazauna garin Ayetoro-Itele a jihar Ogun sun wayi gari da samun wani labarin marar dadi na sumar da wani Malami ta hanyar yi masa fyade da ake zargin wasu dalibai mata guda biyar da aikata wa.

Labarin abin da ya faru ya bayyana ne da safiyar ranar Alhamis bayan wani makusanci ga Malamin da abin ya faru a kansa ya buga wa jami'an 'yan sanda waya domin sanar da su abin da ya faru.

Wani shaidar gani da ido da ya yi ikirarin cewa a kan idonsa 'yammatan suka shiga gidan Malamin, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa matasan 'yammatan, wadanda shekarunsu na haihuwa basu haura 16 zuwa 18 ba, dalibai ne saboda kowaccensu tana dauke da littafin rubutu da na karatu yayin da suka shiga gidan Malamin.

Dalibai mata 5 sun yi wa maa makarantar sakandire, ya sumalaminsu fyade Dalibai mata 5 sun yi wa maa makarantar sakandire, ya sumalaminsu fyade i a gida.

Dalibai mata 5 sun yi wa malaminsu fyade a makarantar sakandire, ya suma
Malami da dalibansa a makarantar sakandire
Asali: Facebook

"Ni a tunanina sun tsara komai kafin zuwansu, domin hatta lokacin da suka zo gidan, kusan kowa ya fita harkokinsa. Da farko ina jin sautin muryoyi daga dakinsa, duk da ban tantance da abin da ake fada ba. Daga baya na fara jin nishi, kamar irin mutum yana wani aiki mai wahala haka. Ban yi tunanin cewa zasu aikata wani abu mai kama da haka ba.

"Bayan 'yammatan sun tafi ne sai na yanke shawarar shiga dakinsa domin ganin halin da yake ciki, amma sai na same shi tsirara, kuma ba a cikin hayyacinsa ba. Nan take na sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Tsugune bata kare ba: An fara yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu sabuwar barazana

An garzaya da malamin zuwa asibiti, inda likitoci da sauran ma'aikatan lafiya suka shiga kokarin ceto ransa, yayin da jami'an 'yan sanda suka fara nasu binciken domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Tuni hukumar makarantar da malamin ke koyar wa ta bayyana cewa a shirye take ta bawa rundunar 'yan sanda hadin kai da dukkan wata gudunmawa da zasu iya bukata yayin binciken da suke gudanar wa.

Kazalika, mahukuntan makarantar sun nuna shakkunsu a kan yiwuwar samun hannun dalibansu a ta'asar da aka aikata wa malamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel