Najeriya ce kasar da nake matukar son zuwa a rayuwata - Lil Wayne

Najeriya ce kasar da nake matukar son zuwa a rayuwata - Lil Wayne

- Sanannen tauraron hip-hop, Lil Wayne ya bayyana bukatarshi ta kawo ziyara Najeriya

- Hakan ya biyo baya ne a cikin makonni kalilan da mawakiyar gwambarar kasar Amurka, Cardi B tazo kasar

- Lil Wayne ya bayyana cewa bai taba koda zuwa nahiyar Afirka ba amma zai so zuwa Najeriya

Tauraron hip-hop, Lil Wayne ya bayyana bukatarshi ta ziyartar Najeriya.

Bukatar nan ta biyo baya ne a makonni kadan bayan da mawakiyar gambarar nan ta kasar Amurka, Cardi B ta kawo ziyara Najeriya.

Mawakin da ya karba kyautukan yabo tare da kambu daban-daban, Lil Wayne ya sanar da manema labarai ne a wani bidiyo cewa bai taba zuwa nahiyar Afirka ba.

KU KARANTA: Google ya bayyana jihohi 10 na Najeriya da 'yan luwadi suka fi yawa a shekarar 2019

A lokacin ne suka tambayeshi ko zai so zuwa, sai yace bai taba zuwa Najeriya ba kuma ita ce kasar da yake son zuwa. Ya ce: "Ban taba zuwa Najeriya ba. Kuma nan nake son zuwa."

Ya kara da cewa zai so ziyarar kasar Egypt kafin daga baya a tambayeshi dalilinshi na son zuwa Najeriya a tattaunawar. Mawakin yace Najeriya waje ne mai cike da nishadi a rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel