Albashi na duk wata N54 ne a matsayin malamin makaranta - Sanata Wamakko

Albashi na duk wata N54 ne a matsayin malamin makaranta - Sanata Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce yana murnar biyansa albashin Naira 54 da ake yi duk wata a matsayin malamin makaranta kafin daga bisani ya zama gwamna a jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai, Sanata Wamakko ya ce har yanzu yana matukar ganin ya bayar da gundun mawa a fanin ilimi duk da cewa ya zama famanen sakatare, mataimakin gwamna kana ya zama gwamna.

Ya ce, "Ni asali ni na malamin makaranta ne kuma ina alfahari da hakan. Na fara aiki a matsayin malami a mataki na uku ina karbar Naira 54 duk wata a matsayin albashi har na zama headmaster, mai duba makarantu, famanan sakatare da sauransu. Na zama mataimakin gwamna, gwamna kuma gashi yanzu na zama Sanata.

"A matsayi na na malami ko principal, na yi imanin cewa ilimi shine abu mafi muhimmanci da za ka iya bar wa al'umma da za su amfana da shi yanzu da ma shekaru masu zuwa.

DUBA WANNAN: Jonathan ya yi karin haske kan batun sake takarar shugaban kasa a 2023

"Ba makarantun frimare kadai na gina ba, na gina makarantun sakandare da makarantun gaba da sakandare biyar a shekaru takwas na mulki na a matsayin gwamna kuma na gina jamiar jiha ta farko a Sokoto."

Sanatan ya bayyana cewa saboda sha'awar ilimi da ya ke yi, ya dauki nauyin sama da dalibai 200 zuwa kasashen ketare domin su yi karatu a fanonin daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel