Jerin wasu Gwamnonin da har yanzu shari’ar su ta ke gaban kotu

Jerin wasu Gwamnonin da har yanzu shari’ar su ta ke gaban kotu

Kawo yanzu akwai shari’o’in zaben da ba a kammala ba a Najeriya. Karar wasu gwamnoni ta na gaban kotun koli a daidai wannan lokaci.

Wani rahoto da Jaridar Daily Trust ta fitar ya bayyana cewa akwai gwamnoni bakwai da su ke sauraron hukuncin da kotun koli za ta yi.

Wadannan jihohi su ne na Adamawa, Bauchi, Benuwai, Imo, Kano, Filato, da Sokoto. A cikinsu dai Kano da Filato ne kawai a hannun APC.

A wannan wata na Junairu ake sa ran za a yanke hukuncin karshe a game da karar da ake yi zaben gwamnonin da aka yi a farkon 2019.

Jibrilla Bindow wanda ya rasa kujerarsa a hannun Ahmadu Fintiri ya daukaka kara da zargin cewa PDP ba ta lashe zaben gwamna a jihar ba.

KU KARANTA: An dage zaman shari’ar Gwamnatin Ganduje da Dattawan Kano

Jerin wasu Gwamnonin da har yanzu shari’ar su ta ke gaban kotu
APC ta na jiran sakamakon shari'ar zaben Sokoto a kotun koli
Asali: Facebook

Shi ma tsohon gwamna Mohammed Abubakar ya na kalubalantar Bala Mohammed a Bauchi kamar yadda ake tuhumar PDP a Benuwai.

A Imo, Hope Uzodimma da sauran ‘Yan takarar hamayya irinsu Ifeanyi Ararume da Uche Nwosu ba su amince da nasarar PDP a zaben 2019 ba.

Haka zalika a jihohin Kano da Sokoto, Abba Yusuf da Aliyu Ahmed sun daukaka kara a kan nasarar da gwamnonin da ke mulki su ka samu.

A jiya ne kotun koli ta ba Gwamnoni Okezie Ikpeazu, Ifeanyi Okowa, Abubakar Bello, da Darius Ishaku gaskiya a hukuncin karar da aka shigar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel