Za a saurari karar Ganduje da Dattawan Kano a 27 ga Watan Junairu a Kotu

Za a saurari karar Ganduje da Dattawan Kano a 27 ga Watan Junairu a Kotu

Wani babban kotu da ke Kano ta sa 27 ga Watan Junairu a matsayin a ranar da za a saurari karar da wasu Dattawan jihar su ka shigar.

Wadannan Dattawa su na kalubalantar kirkiro sababbin masarautu da gwamnatin Mai girma Abdllahi Umar Ganduje ta yi a Kano.

Kamar yadda hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto, Bashir Usman Tofa da wasu mutane 19 ne su ka shigar da karar.

Alhaji Bashir Usman Tofa da sauran masu karar su na kalubalantar kafa sababbin Sarakuna da aka yi a Karaye, Bichi, Gaya da Rano.

Wadanda aka maka a kotu sun hada da: Mai girma gwamna, Kakakin majalisar dokokin Kano, Kwamishinan Shari’a da Masarauta.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya caccaki 'Dattawan Jihar Kano' a kotu

Za a saurari karar Ganduje da Dattawan Kano a 27 ga Watan Junairu a Kotu
Dattawan Kano sun makara wajen sanar da karar da su ka shigar
Asali: Facebook

Sauran wanda ake kara su ne: Tafida Abubakar-Ila, Ibrahim Abdulkadir-Gaya, Dr Ibrahim Abubakar II, da Aminu Ado-Bayero.

Alkali mai shari’a Nura Sagir ya sa wannan rana ne bayan Lauyan masu karar ya nemi kotu ta dage zaman da za ayi zuwa nan gaba.

Babban Lauya A.B. Mahmoud wanda ya tsayawa Dattawan ya ce ba su sanar da wadanda su ke kara game da shari’ar da wuri ba.

A bangare guda, Kwamishinan shari’a, Ibrahim Mukhtar ya koka da yadda aka kawo masu labarin karar mako guda da zuwa Kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel