Majalisar Amurka za ta takawa Trump burki wajen fada da kasar Iran

Majalisar Amurka za ta takawa Trump burki wajen fada da kasar Iran

‘Yan Majalisar Wakilan tarayyan kasar Amurka sun nuna cewa ba za su bari shugaban kasa Donald Trump ya tafi yaki da Iran ba.

Jam’iyyar hamayya ta Democrat wanda ta fi rinjaye a majalisar wakilai ta bayyana cewa za ta kada kuri’ar rashin goyon bayan yaki.

Kakakin majalisar Amurka, Nancy Pelosi, ta ce ‘Yan jam’iyyarta a majalisa za su dauki mataki domin ganin kasar ba ta jawo yaki ba.

Pelosi ta shaida cewa Sakataren gwamnatin Amurka, Mike Pompeo bai duba bukatun da su ka gabatar masa a zaman da su ka yi ba.

“Shugaban kasa ya tabbatar da cewa bai da takamaimen tsarin da zai bi wajen tsare mutanen Amurka, da kawo zaman lafiya da Iran.”

KU KARANTA: Kan Shugaban Amurka Donald Trump zai yi kudi a kasar Iran

Majalisar Amurka za ta takawa Trump burki wajen fada da kasar Iran
Sanatocin Jam’iyyar Trump su ke da rinjaye a majalisar dattawa
Asali: UGC

Misis Pelosi ta cigaba da cewa Trump bai san yadda zai shawo kan tashin hankalin da ya ke neman barkewa tsakanin Amurka da Iran ba.

A cewar ta: “Dole gwamnati ta sanar da majalisa game da wani yunkurin zuwa yaki, amma Trump ya yi gum kan kisan Qasem Soleimani.”

A dalilin wannan danyen aiki da Trump ya yi ba da sanin ‘Yan majalisa ba ne, ake shirya taka masa burkin shiga wani yaki da kasar ta Iran.

Shugabar majalisar ta kuma nuna cewa su na tunanin karbe ikon da aka ba shugabannin Amurka na tada Dakarun soji ba da sanin majalisa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel