Majalisar dinkin duniya ta tsoma baki a rikicin Amurka da Iran
A yayin da kasar Iran ta fara kai hare - haren daukar fansa a kan kasar Amurka, majalisar dinkin duniya (UN) ta ci al washin cigaba da shiga tsakanin kasashen biyu domin ganin cewa an samu lafawar gangunan yaki da kowanne ke buga wa.
An dade ana nuna yatsa a tsakanin kasar Amurka da Iran kafin daga bisani su fara takalar junansu da yaki.
A 'yan kwanakin baya bayan nan ne kasar Amurka ta kashe babban hafsan rundunar sojojin kasar Iran, Janar Qassem Soleimani, a wani hari da ta kai masa a kasar Iraq ta hanyar amfani da wani jirgin yaki mai layar zana da ake sarrafa shi daga nesa ta na'ura mai kwakwalwa.
A ranar Laraba ne babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya sanar da cewa zai cigaba da tattauna wa da kasashen biyu domin ganin an samu lafawar amon gangunan yaki da kowanne bangare ke buga wa.
Kalaman na Guterres na zuwa ne kwana daya kacal bayan kasar Iran ta kaddamar da wasu hare - hare da makamai masu linzami a wasu sansani guda biyu na sojojin kasar Amurka dake kasar Iraqi.
Hare - haren da kasar Iran ta kai wa sansanin sojin kasar Amurka na zuwa ne bayan wasu sa'o'i da binne gawar janar Soleimani.
DUBA WANNAN: Sabbin masarautu: Ganduje ya kalubalanci dattijan Kano a gaban kotu, ya ce akwai mutum miliyan 20 a Kano
A wani jawabi da mai magana da yawunsa ya fitar, Guterres ya jaddada tsananin bukatar neman zaman lafiya.
"ku daina rura wutar yaki, ku saurara haka, ku fara sabuwar tattauna wa da sabunta hadin kanku na kasa da kasa.
"Alhakin dukkanmu ne mu tabbatar da cewa ba a samu barkewar yaki ba, kasashen duniya ba zata zuba ido suna gani hakan ta faru ba," a cewarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng