Zamfara: Tubabbun 'yan bindiga sun yi taro a daji, sun yanke shawarar mataki na gaba

Zamfara: Tubabbun 'yan bindiga sun yi taro a daji, sun yanke shawarar mataki na gaba

Shugaban tubabbun 'yan bindigar jihar Zamfara ya sadu da gwamnan jihar a daji don kara duban yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi da Gwamna Muhammad Matawalle a watan Yuni na shekarar da ta gabata, cewar kwamishinan 'yan sanda, Usman Nagogo.

Nagogo, wanda ke bayyana nasarorin da aka samu a yarjejeniyar zaman lafiyan wacce ta wanzu a watanni bakwai da ya gabata, yace wasu daga cikin manyan tubabbun masu suna Muhammadu Bello da kuma Halilu da sauran shugabannin duk sun hallara a dajin, tare da alkawarin maganin sauran da basu yada makamai ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Taron ya samu hallarar manyan shugabannin hukumomin tsaro, shugaban tubabbun 'yan bindigar, kwamishinan tsaro da cikin gida na jihar, Alhaji Abubakar Dauran da sauran masu ruwa da tsaki.

"Tun farko dai tubabbun 'yan bindigar sun sanar da jami'an tsaro a kan taron da zasu yi a daji don haka aka sanar da jama'a gudun kada su tsorata don ganin kai kawo dinsu. Sun kuma tabbatar da bada goyon bayan zaman lafiya a jihar," in ji shi.

DUBA WANNAN: Matasa sun yi zanga-zanga kan sakin wasu masu garkuwa da mutane a Adamawa

"Bari in baku misali, wani dan bindiga tubabbe ya kashe wani wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne a kauyen Munhaye dake karamar hukumar Tsafe ta jihar. Tubabben dan bindigar ya samu wata bindiga daga hannun wanda ake zargin kuma ya mika ta ga ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar," ya kara da cewa.

Shugaban 'yan sandar jihar ya kara da bayyana cewa, an sako wasu mutane 500 da aka yi garkuwa dasu kuma duk ta hanyar tattaunawar da aka yi da 'yan bindigar. Ya ce hukumar 'yan sandan jihar zata samo hanyoyi hudu na cigaba da inganta tsaro.

Shugaban 'yan bindigar na jihar ya tabbatar da zancen Nagogo kuma sun hadu a wani daji dake kusa da Tubali a karamar hukumar Shinkafi ta jihar. Sun bayyana cewa zasu dau mataki na gaba wanda zai tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel