Jami'an EFCC na can gidan Shehu Sani suna binciken kwakwaf

Jami'an EFCC na can gidan Shehu Sani suna binciken kwakwaf

Labaran da Legit.ng ta samu daga jaridar The Cable na nuni da cewa yanzu haka jami'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) suna can gidan tsohin sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Kwamred Shehu Sani, suna gudanar bincike.

Jami'an hukumar EFCC sun dira gidan tsohon Sanatan dake unguwar Wuse II a Abuja da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, 2020.

A makon jiyanne hukumar EFCC ta cafke Shehu Sani bisa zarginsa da zambar wani dan kasuwa a Kaduna makudan miliyoyi.

Tuni tsohon Sanatan ya bayyana cewa wasu makiyansa na siyasa ne suka tunzura dan kasuwar har ya shigar da korafinsa a ofishin EFCC domin kawai a tozarta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng