Yan PDP 30,000 sun sauya sheka zuwa APC a Zamfara

Yan PDP 30,000 sun sauya sheka zuwa APC a Zamfara

- Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 30,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara

- Wadanda suka sauya shekar sun kasance masu biyayya ga Alhaji Ibrahim-Shehu Bakauye, tsohon dan takarar gwamna na PDP, wanda ya koma jam’iyyar APC kwanan nan

- Masu sauya shekar karkashin jagorancin Shugaban PDP na bangaren adawa a jihar, Nasiru Milo da mambobi daga kananan hukumomi 14 na jihar sun sanar da sauya shekarsu a sakatariyar APC na jihar da ke Gusau

Akalla sama da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 30,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa wadanda suka sauya shekar sun kasance masu biyayya ga Alhaji Ibrahim-Shehu Bakauye, tsohon dan takarar gwamna na PDP, wanda ya koma jam’iyyar APC kwanan nan bayan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar, Alhaji Abdul’aziz Yari.

An tattaro cewa Bakauye, tsohon dan majalisa mai wakiltan Gusau/Tsafe a majalisar dokokin tarayya daga 2011 zuwa 2015, ya kasance dan takarar gwamna a PDP a zaben 2019 amma sai ya sha Kaye a hannun Gwamna Bello Matawalle a zaben fidda gwani.

KU KARANTA KUMA: Shugaban PDP ya yanke jiki ya fadi matacce a Kogi

Masu sauya shekar karkashin jagorancin Shugaban PDP na bangaren adawa a jihar, Nasiru Milo da mambobi daga kananan hukumomi 14 na jihar sun sanar da sauya shekarsu a sakatariyar APC na jihar da ke Gusau, babbar birnin jihar a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng