Shugaban PDP ya yanke jiki ya fadi matacce a Kogi

Shugaban PDP ya yanke jiki ya fadi matacce a Kogi

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na Kogi ta yamma, Mista Taiwo Kola-Ojo ya mutu.

Ojo ya yanke jiki ya fadi sannan ya mutu a yammacin ranar Talata, 7 ga watan Janairu yayinda ya ke buga wasan Kwallo na tennis.

Babban sakataren PDP na jihar Kogi, Bode Ogunmola wanda ya tabbatar da mutuwar a wani jawabi a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu ya bayyana mutuwar Kola-Ojo a matsayin abun bakin ciki kuma wanda ya zo a bazata.

Jawabin ya ce Shugaban PDP din ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaba da nasarar jam’iyyar a jihar kuma cewa za su yi kewarsa.

Jam’iyyar ta PDP ta yi addu’an Allah ya ba iyalansa da mambobin jam’iyyar hakurin rashinsa.

KU KARANTA KUMA: Iran ta ce Amurkawa 80 aka kashe a harin makamai masu linzami da ta kai

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Allah ya yiwa zababben shugaban kwamitin rikon kwarya a yankin karamar hukumar Ipokia da ke jihar Ogun, Saibu Adeosun Mulero rasuwa.

Ya rasu ne yan sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin jihar ta tantance shi.

Ya kasance daya daga cikin zababbun shugabannin kwamitin mika mulki na kananan hukumomi 20 a jihar Ogun, wadanda Gwamna Dapo Abiodun ya nada a makon da ya gabata.

An tattaro cewa marigayin ya shirya tsaf domin tantancewar da za a yi masa a Abeokuta amma sai ya dan kwanta, baccin da bai tashi ba kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel