Idan Trump ya ya sake kai mana hari, zamu ragargaji Izra'ila da Dubai - Iran

Idan Trump ya ya sake kai mana hari, zamu ragargaji Izra'ila da Dubai - Iran

- Iran ta harba rokoki 20 sansanin Soji Amurka dake Iraqi

- Ta yi gargadin cewa idan har Amurka ta sake kai mata hari, Izra'ila ba zata ji da dadi ba

- Hukumar tsaron Iran ta sanar da hakan a tashar talabijin

Kasar Iran ta yi barazanar ragargazan Izra'ila da Dubai idan har kasar Amurka ta sake kai mata kara bayan ta mayar da martani da daren jiya inda ta kaiwa Sojin Amurka hari.

Iran ta harba rokoki 20 sansanin Sojin Amurka dake Iraqi domin mayar da martani kan kisan babban kwamandan Iran, Qassem Soleimani, da Amurka tayi ranar Juma'a.

Sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad ne aka harba manyan rokokin misalin karfe 5:30 na yammacin Talata kuma da alamun akalla sojojin Amurka 80 sun hallaka.

Hukumar tsaron Iran ta gargadi Amurka kan kokarin ramawa.

Sun sanar da hakan ne ta wabi jawabi a tashar gwamnatin Iran IRNA.

"Muna gargadin dukkan abokan Amurka, wadanda ke baiwa Sojojin yan ta'adda (Amurka) daman amfani da kasashensu cewa duk inda Amurka tayi amfani da shi wajen kawo mana hari zamu ragargajeta."

Wani tashan talabijin na daban ta yi barazanar ragargazan kasar Izra'ila da Dubai.

Kalli bidiyon harin:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel