An yi kwana da kwanaki ba a ji daga bakin Shehu Sani a kafafen sadarwa ba

An yi kwana da kwanaki ba a ji daga bakin Shehu Sani a kafafen sadarwa ba

A halin yanzu an shafe kusan mako guda ba aji duriyar Shehu Sani a kan kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta na zamani ba.

Ba kasafai aka saba daukar dogon lokaci jama’a masu bibiyar kafofin sadarwa ba su ji daga bakin tsohon Sanatan na jihar Kaduna ba.

Sanatan ya yi kusufi ne a daidai lokacin da hukumar EFCC ta ke zarginsa da laifin karbewa wani hamshakin ‘Dan kasuwa dalolin kudi.

Jaridar The Cable ta yi bincike ta gano cewa a baya, duk rana ta Allah, Sanatan ya kan yi magana a shafinsa na Tuwita fiye da sau guda.

A Watan Disamban shekarar bara kawai, fitaccen ‘Dan gwagwarmayar ya yi magana a dandalinsa na Tuwita na @ShehuSani sau 103.

KU KARANTA: An yi ram da wani hamshakin 'Dan kasuwa a Garin Kaduna

Sani ya cigaba da maganganun da ya saba har zuwa Ranar karshe ta shekarar 2019, ya na mai sa ran cewa gaba za ta yi wa Najeriya kyau.

Tun daga wannan lokaci da Sanatan ya yi magana game da shekaru goman baya da aka shafe, bai sake lekowa dandalin Tuwita da Facebook ba.

Haka zalika ‘Dan siyasar ya kan wallafa duk abin da ya rubuta a shafinsa na Tuwita a kan dandalin sa na Facebook inda ya ke da Mabiya.

Ana zargin tsohon ‘Dan majalisar dattawan da karbar kudi wajen Alhaji Sani Dauda da nufin zai sa baki a shari’ar da ake yi da shi a gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng