Kasar Iran ta kai wa wasu Dakarun Sojojin Amurka da ke Iraqi hari

Kasar Iran ta kai wa wasu Dakarun Sojojin Amurka da ke Iraqi hari

Kasar Iran ta harba wasu makamai da-dama zuwa kasar Iraki kamar yadda mu ka samu labari da safiyar Ranar Laraba, 8 ga Watan Junairu, 2020.

Iran ta saki makamai masu linzami ne zuwa wasu sansani biyu na Dakarun sojojin Amurka da ke kasar Iraki, a matsayin ramuwar gayya ga kasar.

Idan ba ku manta ba, kasar Amurka ta kashe babban Sojan da Iran ta ke ji da shi watau Janar Qasem Soleimani, wanda hakan ya jawo rikici.

CNN ta bayyana cewa babu cikakken rahoto kawo yanzu game da adadin mutanen da su ka mutu ko su ka jikkata a sakamakon wannan sabon hari.

Kawo yanzu dai ana kokarin binciken ta’adin da harin ya yi ne kamar yadda labari ya zo mana, yayin da ake cigaba da zama cikin halin dar-dar.

Jami’an kasar Iraqi sun shaidawa ‘Yan jarida cewa ba a samu wani Sojan kasar da ya mutu ko ya samu rauni a sakamakon wannan hari na dazu ba.

KU KARANTA: Trump ya dawo daga rakiyar kai wa wuraren tarihin Iran hari

Ko da babu wani jawabi da ya fito daga bakin hukumomin Amurka, shugaban kasa Donald Trump, ya tabbatar da harin, sannan ya ce zai yi jawabi.

Sakataren gwamnatin Amurka, Mike Pompeo ta Ministan tsaro, Mark Esper sun gana da shugaba Donald Trump a fadar shugaban kasar bayan harin.

Trump ya ce: “Lafiya lau! An harbo makami masu linzami daga Iran zuwa sansanin Sojojin mu biyu a Iraki. Ana duba barnar da aka yi. Babu komai.”

“Mu mu ka fi kowa karfin makamai da Sojoji a Duniya nesa ba kusa ba. Zan yi jawabi gobe da safe.” Inji Shugaban Amurkan a shafinsa na Tuwita.

Wani Ministar kasar Iran, ya bayyana cewa yunkurin kare kai ta sa su ka kai wannan danyen hari. A cewarsa, Iran ba kokarin jawo yaki su ke yi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel