Wasika zuwa ga Buhari: Sojoji sun yi barazanar janye wa daga yaki da Boko Haram, sun bayyana dalilansu

Wasika zuwa ga Buhari: Sojoji sun yi barazanar janye wa daga yaki da Boko Haram, sun bayyana dalilansu

Wasu dakarun rundunar soji dake aiki da bataliya ta 159 a garin Geidam, jihar Yobe, sun yi barazanar janye wa daga wurin aikinsu saboda zargi wofantar da su da suka ce manyan mahukunta a rundunar soji sun yi.

A wata wasika da suka aika wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, majalisar tarayya, majalisar dinkin duniya da wasu hukumomin kasa da kasa, sojojin sun bayyana bacin ransu bisa yadda suka ce an jibge tare da manta wa dasu a yankin arewa maso gabas mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram.

Dakarun sojin, wadanda suka ce a baya sun yi aiki a rundunar sojojin kasa da kasa a kasar Liberia, sun bayyana cewa manyan sojoji a rundunar soji sun yi burus da halin da suke ciki saboda kwadayi da son rai.

Sun kara da cewa hatta hankulan iyalansu dake gida ya kasa kwanciya saboda fargabar da suka shiga sakamakon dadewar mazajensu a filin dagar yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

"Muna masu sanar da kai cewa mun dade fiye da ka'ida a yankin arewa maso gabas.

"An fara kawo mu wannan yanki ne a ranar 10 ga watan Yuli, 2010, domin yaki da kungiyar Boko Haram, bayan mun dawo daga kasar Liberia.

Wasika zuwa ga Buhari: Sojoji sun yi barazanar janye wa daga yaki da Boko Haram, sun bayyana dalilansu
Sojoji
Asali: UGC

"Mune yanzu haka muke kula da garuruwan Dapchi, Bamari, Kanama zuwa iyaka da jamhuriyar Nijar.

"Wannan ita ce shekarar mu ta hudu a cikin yanayin yaki da 'yan Boko Haram, amma har yanzu ba a sauya mu ba duk da an sauya bataliya da dama da suka zo a bayanmu. Rundunar mu ce tafi kowacce dadewa a yankin arewa maso gabas, " kamar yadda suka bayyana a cikin wasikar.

DUBA WANNAN: Shekau ya mayar wa da gwamna Zulum martani, ya zarge shi da rashin sanin Al-Qur'ani

Sojojin, wadanda suka ce an dauko su ne daga bataliyar sojoji ta daya dake jihar Kebbi, sun bayyana cewa sun yi wa babban hafsan rundunar soji korafi, amma kuma har yanzu shiru duk da alkawarin duba lamarinsu da ya yi.

Sojojin sun dora alhakin rashin yi musu sauyin da cin hanci da son rai a tsakanin mahukunta a rundunar sojin Najeriya, kuma a saboda haka ne suka yanke shawarar neman taimako ta hanyar mika kukansu wurin da za a share hawayensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel