Abin da ya sa farashin waya da ‘data’ zai tashi sama Inji ALTON

Abin da ya sa farashin waya da ‘data’ zai tashi sama Inji ALTON

Zai iya zama dole ga kamfanonin sadarwan da ke aiki a Najeriya su kara kudin sayen data na hawa yanar gizo da kuma farashin yin wayar salula.

Kamfanonin za su zama babu yadda su ka iya sai sun kara farashinsu ne a dalilin wani mataki da gwamnatocin jihohi su ka dauka kwanan nan.

Gwamnoni akalla 14 ne su ka kara farashin RoW da kamfanonin sadarwan su ke biya domin jan layukan tarhon su da ke karkashin kasa a jihohin.

Kungiyar ALTON ta kamfanonin sadarwan da ke aiki a Najeriya sun yi gargadi cewa zai zama dole su kara kudi saboda karin da aka yi masu.

Shugaban kungiyar ALTON na kasa, Gbenga Adebayo ya koka da cewa harajin da hukumomin Najeriya su ke lafta masu ya yi yawa a fadin kasar.

KU KARANTA: Minista Pantami ya ce a dakatar da sakon Voice Mail na kai-tsaye

Abin da ya sa farashin waya da ‘data’ zai tashi sama Inji ALTON
Kudin waya da hawa yanar gizo na iya tashi saboda kara kudin RoW
Asali: Twitter

Jihohin da su ka kara wannan kudi na RoW su ne: Legas, Kano, Anambra, Ondo, Kuros-Riba, Kogi, Osun, Kaduna, Enugu, da kuma jihar Adamawa.

Sauran gwamnonin da su ka yi wannan kari sun hada da na: Ebonyi, Imo, Kebbi da jihar Gombe kamar yadda mu ka samu labari daga The Nation.

A wadannan Jihohi 14, an kara farashin RoW ne daga N300 ko N500 kan kowane mita zuwa N3, 000 har N6, 000, domin karin samun kudin shiga.

Kamfanonin sadarwan su na bukatar RoW na kilomita mai yawa saboda karfin layinsu ya iya kai wa kowane lungu da sako domin su yi ciniki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel