Sanata Shehu Sani ya ki hawa na’urar ‘Polygraph’, ya nemi ya rantse da Kur’ani

Sanata Shehu Sani ya ki hawa na’urar ‘Polygraph’, ya nemi ya rantse da Kur’ani

Ana ta fama tsakanin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa da kuma Shehu Sani da ake zargi da laifi.

Hukumar EFCC ta na zargin Sanata Shehu Sani da laifin yi wa wani fitaccen ‘Dan kasuwa a Garin Kaduna kwace na kudi har Dala 24, 000.

Jami’an EFCC sun bukaci Shehu Sani ya yi amfani da na’urar ‘yar nune wanda ke tona asirin makaryaci, amma ya ce sam ba zai yi ba.

Tsohon Sanatan kasar ya nuna cewa sai dai ya yi rantsuwa da littafin Al-Kur’ani mai tsarki a kan ya yi amfani da na’urar nan ta Polygraph.

Shugaban kamfanin motoci na ASD watau Alhaji Sani Dauda shi ne ya kai ‘Dan siyasar gaban EFCC, kuma ya ki janye wannan karar.

KU KARANTA: Ban taba ganin Shehu Sani a rayuwa ta ba - Alkalin Alkalai

Yanzu an dauke tsohon Sanatan daga wani dakin da ya ke tsare zuwa babban ofishin EFCC da ke Unguwar Wuse domin cigaba da bincikensa.

A nan ne aka yi ta faman arba da Sani, ya ce: “Ba zan yi gwajin ba, ban yarda na na’urar ba. Ban tabbatar ko ya na aiki yadda ya kamata ba.”

“A maimakon na’urar, ku ba ni Kur’ani mai tsarki in rantse da shi.” Jami’an EFCC dai ba su tursasa masa ba, sai dai aka rubuta abin da ya fada.

Wannan na’urar zamani ta kan gane idan mutum ya na karya ne ta hanyar auna hawan jini da bugun zuciya da numfashi da wasu alamomi.

Ana sa ran cewa zuwa Ranar Laraba, 8 ga Watan Junairu, 2020, za a yi amfani da na’urar a kan Iyalin Alhaji Sani Dauda, wanda ya kawo karar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel