Tanko Yakasai ya caccaki Buhari da APC, ya ce babu abunda ya chanja a Najeriya tun 2015

Tanko Yakasai ya caccaki Buhari da APC, ya ce babu abunda ya chanja a Najeriya tun 2015

Wani jigon arewa kuma wanda ya kafa kungiyar dattawan arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tabarbarewar wutar lantarki a Najeriya.

A wasu jawabai da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, Channels TV ta ruwaito cewa Yakasai ya bayyana cewa duk da ikirarin chanji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), babu abunda ya chanja tun 2015.

Yakasai ya bayyana cewa shekaru shida bayan Buhari ya zama Shugaban kasar Najeriya, kasar ba ta da wani abun nunawa.

Ya ce: “A lokacin da APC ta gabatar da Buhari, sun zo da taken ‘chanji’. Don haka a yanzu mun samu APC da Buhari a mulki; muna a shekara ta biyar yanzu, babu chanji a nawa ra’ayin.

"Ku duba lamarin wutar lantarki a kasar, ku duba komai; wani chanji aka samu tun daga 2015 zuwa yanzu? Idan mutane suka zo da take, ku tursasa masu yin bayani don mu samu hujjar rike su kan alkawarin su. Shekara daya da ya gabata, Ina cin moriyar wutar lantarki na kimanin sa’o’i 8-12 a gidana na Kano. A yau ya koma sa’o’i 6.

KU KARANTA KUMA: Bam ya kashe mutane 30 a wata gada mai cike da jama’a a Borno

“Masu kudi ne kawai ke da ikon zama yan takara saboda mara kudi ba zai iya zama dan takara ba a yau. Duk wani da zai nemi kujerar gwamnati ko wani mukami yana yin hakan ne da karfin aljihunsa."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel