Yin rajista sau biyu: INEC ta bayyana matakin da za ta dauka kan Gwamna Yahaya Bello

Yin rajista sau biyu: INEC ta bayyana matakin da za ta dauka kan Gwamna Yahaya Bello

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa za ta gabatar da Gwamna Yahaya Bello a gaban kuliya saboda rajistan da ya yi sau biyu idan wa'adin mulkinsa ya kare.

A cewar kwamishinan wayar da kan mazu zabe da watsa labarai na kasa na hukumar, festus Okoye, kariyar da doka ta bawa Yahaya Bello a matsayinsa na gwamna ne dalilin da yasa ba za a iya taba shi yanzu ba.

Ya kuma bayyana cewa hukumar zaben ta yanke shawarar shigar da karar Yahaya Bello ne bayan binciken da ta yi a kansa har ta kori wasu daga cikin jami'anta biyu tare da dakatar da wani Mataimakin Direkta.

Okoye ya ce; "Ba muyi watsi da binciken da muke gudanarwa ba a kan gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ba a kan batun yin rajista sau biyu amma babu abinda za mu iya yi a yanzu saboda kariyar da doka ta bashi. Amma da zarar kariyar ta gushe, hukumar za ta dauki mataki kan abinda za ta yi a kansa.

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

"Mun fara da daukan mataki a kan ma'aikatan mu da muka muka samu da hannu a lamarin yayin da muke jira zuwa lokacin da wa'adin mulkin gwamnan zai kare domin ita ke ba shi kariya."

Da aka masa tambaya a kan cewa ko binciken da suka gudanar ya nuna cewa gwamnan Kogin yana da laifi, kwamishinan na INEC ya ce.

"Akwai matakai da dama, sai ka fara yin bincike, sannan ka gabatar a gaban kotu sannan a tabbatar da laifi ko a wanke wanda ake zargin. Ba za ka iya yanke hukunci ba kafin ta gama bin matakan. Saboda haka za mu sani idan mun kai wannan gabar".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel