Bana nan bana chan: Ni dan APC ne, inji Gwamnan PDP

Bana nan bana chan: Ni dan APC ne, inji Gwamnan PDP

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya caccaki mambobin jam’iyyar Peoples Democracy Party (PDP) da ke shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), cewa shi dan APCne dari bisa dari.

Umahi wanda ya yi magana lokacin da mutanen Yankunan Ishielu da Onicha suka ziyarce shi a lokacin bikin Kirsimeti, ya bukaci irin wadannan mutane da su “daina yawo daga wannan jam’iyyar zuwa wancan” domin za a iya kama su da laifin cin dunduniyar jam’iyya.

Ya ce: “Ku tsaya a wui guda. Kada ku gudu daga nan zuwa chan ko daga chan zuwa nan. Ba wani tasiri da hakan zai yi. Idan ka ce kana chan (APC), ka sani ina chan tun tuni. Idan ka je APC, ni dan APC ne, idan ka je PDP, ina chan shima.

“Ni kadai ne nake abunda ya saba jam’iyya kuma babu abunda zai faru. Duk wasu da suka yi abunda ya saba jam’iyya sun yi waje. Don haka, ina wakiltanku a APC yayinda dukkanku ke ci gaba da kasancewa a PDP. Idan kun so, ku je ku rubuta a kafofin sadarwa.”

Gwamnan ya bibiyi ikirarinsa na kasancewa dan APC ta hanyar fadin cewa ya aika goron Kirsimeti ga shugabannin jam’iyyar mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani

Ya yi godiya ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sanya Ebonyi cikin jerin jihohin da za su samu kwalejin ilimi na tarayya, wacca ita kadai ce ta samu shiga a yankin kuu maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel