Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani

Kungiyar yan’uwa Musulmai na Shi’a a Najeriya wacce aka fi sani da Islamic Movement in Nigeria (IMN) a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, ta jagoranci wani tattaki hanyar Banex, yankin Wuse har zuwa shataletalen Burger a babbar birnin tarayya, Abuja.

Mambobin na IMN na zanga-zanga ne akan kisan babban kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani biyo bayan wani hari da kasar Amurka ta kai Kansa a ranar Juma’a da ya gabata.

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani
Source: Twitter

Mambobin kungiyar na kuma neman a saki shugabansu El-Zakzaky da matarsa, Zeenat wadanda ke tsare a hannun hukumar DSS a jihar Kaduna.

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani

Yan shi’a sun yi zanga-zanga, sun kona tutar Amurka kan kisan Soleimani
Source: Twitter

Fusatattun masu zanga-zangan sun fito unguwannin Abuja, suna wakokin sukar gwamnatin Amurka.

KU KARANTA KUMA: An harbe jami’an yan sanda 2 a wani harin bazata da Boko Haram ta kai

Sun kuma kona tutar Amurka sannan sun kasance dauke da allunan sukar kisan babban janar din Iran.

A baya mun ji cewa babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an Yansandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam.

IG Adamu ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan kisan wani babban kwamandan yaki na kasar Iran da gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a makon da ta gabata, inda yace sun samu labarin akwai wasu dake shirin tayar da hankulan jama’a a Najeriya tare da yi ma gwamnatin Najeriya zagon kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel