Soja ya kashe mutane biyu da sharbebiyar wuka, ya raunata wasu da yawa a cikin barikin sojoji

Soja ya kashe mutane biyu da sharbebiyar wuka, ya raunata wasu da yawa a cikin barikin sojoji

Wani sojan Najeriya dake hutun zaman jinya a gidansa dake cikin barikin sojoji ya kashe mutane biyu tare da raunata wasu da dama yayin da ya shiga sukar duk wanda ya gani da wata sharbebiyar wuka.

Sojan mai suna Olodi Blessed dake aiki da rundunar sojin Najeriya a jihar Osun ya kashe wani abokin aikinsa soja da kuma makwabcinsa a cikin barikin.

Kazalika, ya raunata matarsa tare da sauran wasu mutane hudu da suka hada da wani soja mai mukamin kofur.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa majiyarta ta shaida mata cewa an garzaya da mutanen da ya raunata zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.

Premium Times ta rawaito cewa an tabbatar da mutuwar mutane biyu; wata mata mai suna Iyabo da soja mai mukamin kofur, daga cikin mutanen da tsautsayin sojan ya fada wa.

Soja ya kashe mutane biyu da sharbebiyar wuka, ya raunata wasu da yawa a cikin barikin sojoji

Sojoji
Source: Facebook

Daga cikin wadanda sojan ya raunata akwai wani soja da ya yi kokarin kwace wukar dake hannun sojan.

Sojan ya yi amfani da wata wuka ta musamman (jack knife) wajen wajen aikata wannan aika-aika da misalin karfe na daren ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Mutane 8 masu karfin iko a gwamnatin Buhari

Daga baya, dandazon sojojin dake zaune a barikin sun samu nasarar cafke sojan tare da tsare shi.

Majiyar Premium Times ta tabbatar da cewa sojan da ya aikata laifin, ya zo hutun zaman jinya ne daga rundunar sojojin dake yaki da 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel