Justice Obasi: Shugaban ‘Yan Sandan Enugu ya bada umarni ayi bincike

Justice Obasi: Shugaban ‘Yan Sandan Enugu ya bada umarni ayi bincike

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na reshen jihar Enugu sun tsare wasu Jami’ansu uku da ake zargi da zaluntar wani Mutumi mai suna Justice Obasi duka.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Ahmed Abdur-rahman ya bada umarni a gudanar da cikakken bincike game da zaluntar wannan Bawan Allah da aka yi.

CP Ahmad Abdur-rahman ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun ‘Yan Sandan Enugu, Ebere Amaraizu, a babban birni Garin Enugu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan a jawabin na sa na Ranar 5 ga Watan Junairu, 2019, ya tabbatar da cewa ya samu labarin abin da ya faru ne a wani bidiyo.

“Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na reshen jihar Enugu su na so su sanar da jama’a cewa idanunta sun kai ga wani bidiyo da ka yawo a Gari…”

KU KARANTA: An rasa wasu Sojojin Najeriya a wani hari da aka kai a Neja

Justice Obasi: Shugaban ‘Yan Sandan Enugu ya bada umarni ayi bincike

Shugaban ‘Yan Sandan Enugu zai binciki bidiyon da ke yawo a Gari
Source: UGC

“…Inda wasu Jami’an 'Yan Sanda su ka sabawa dokar aiki su ka doki wani Justice Obasi a Ranar 4 ga Watan Junairun 2020 a hanyar Kenyatta Uwani.”

“Mu na son sanar da jama’a cewa wannan danyen aikin da aka ga Jami’an sun yi, ya sabawa aikinmu, kuma mu na Allah-wadai da wannan.”

“A nan ne, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Enugu ya bada umarni ayi bincike na musamman game da abin da ya faru, domin hukunta masu laifin”

DSP Amaraizu ya shaidawa ‘Yan jarida an kama wadannan Jami’an tsaro da su ka yi ba daidai ba, kuma an garkame su kamar yadda IGP ya bada umarni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel