Manyan Jam’iyyar PDP sun fara yakin neman takarar 2023 tun yanzu

Manyan Jam’iyyar PDP sun fara yakin neman takarar 2023 tun yanzu

Rahotanni su na zuwa mana cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar hamayya ta PDP sun soma aiki ta karkashin kasa domin su samu takara a zaben 2023.

Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan ‘Yan adawa sun fara neman hanyar samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa ne a zabe mai zuwa.

Wani babba a cikin jam’iyyar ta PDP ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa mafi yawan wadanda su ka nemi tikiti a 2019, za su nemi su sake fitowa.

Sai dai wadannan ‘Yan siyasa su na ta faman harin 2023 ne yayin da jam’iyyar ba ta kai ga cin ma matsaya kan yankin da zai fito da ‘Dan takara ba.

Kawo yanzu akwai fastoci na tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso, su na yawo a kafafen yada labarai na zamani, wanda ke nuna ya na harin 2023.

KU KARANTA: Masu rike da madafan iko a Gwamnatin Shugaba Buhari

Manyan Jam’iyyar PDP sun fara yakin neman takarar 2023 tun yanzu

Akwai wadanda su ka kai ga neman tikitin zabe mai zuwa a yanzu
Source: Twitter

A daidai wannan lokaci kuma wasu Matasa sun huro wuta cewa zai PDP ta sake kai takarar shugaban kasa zuwa Arewa maso Gabas a zabe na gaba.

Wani wanda ya ke cikin majalisar NEC ta jam’iyyar hamayyar, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wannan hanzari da wasu ke yi, zai iya jawo masu sabani.

A cewarsa, jam’iyya ta rubuta takarda zuwa ga hukumar DSS domin ta binciki wadannan ‘Yan siyasar na ta da ke neman riga Malam zuwa masallaci.

Akwai kishin-kishin din cewa Cif Bode George wanda ya na cikin manyan jam’iyyar a Kudancin Najeriya, ya kammala shirin kaddamar da takararsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel