Hunturu: Yadda garwashin dumama daki ya halaka samari biyu

Hunturu: Yadda garwashin dumama daki ya halaka samari biyu

Wasu matasa masu shekaru 24 zuwa 25 sun rasa ransu sakamakon kai garwashin wuta daki don jin dumi a Jos, jihar Filato. Sun yi hakan ne sakamakon tsananin sanyin da ya addabi jihar da sauran sassan kasar nan.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, mamatan masu suna Saminu da Idris sun rasu ne a daren Juma’a bayan da suka kai garwashi dakinsu, a kokarinsu na dumama jikinsu saboda sanyi.

Babban yayan daya daga cikin mamatan, Labiru Idris, wanda a gidansa mummunan lamarin ya auku, ya sanar da manema labarai cewa su biyun sun dawo wajen karfe 11 na dare, inda suka kwankwasa masa kofa don karbar kasko da gawayi.

Kamar yadda yace, a lokacin da ya tashi da safe sai yaji kauri na fitowa daga cikin gidan. “Na duba madafi ina tunanin ko matata ce ta bar wani kayan wuta a kunne, amma sai na gano cewa ba daga nan kaurin ke fitowa ba.” ya bayyana.

DUBA WANNAN: Kishi: Yadda wata mata ta tura kishiyarta cikin rijiya

Idris ya kara da cewa, “bayan tsananta bincike ne na gano cewa kaurin daga dakin kanina yake. Na leka ta taga amma hayaki ne kawai ke fita. Na kira sunan kanin nawa amma shiru. Daga nan sai na kira makwabcina wanda ya taya ni tura kofar, amma sai muka tarar da dukkansu sun rasu.

“A tunani na, wannan hayakin ne daga garwashin ya turnike dakin, ya hana su iska mai kyau. Mun tarar da abokin kanin nawa a kusa da kofa. Hakan na nuna cewa ya yi yunkurin bude dakin amma sai gobara ta kama, wacce ta cinyesu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng